Malami ya karyata zargin ba DCP Kyari gaskiya, ya yi karin haske


Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami ya karyata rade-radin da yake yawo na cewa ya wanke DCP Abba Kyari.

Jaridar Tribune ta rahoto Abubakar Malami SAN yana mai karin haske a kan matsayarsa.

Ministan ya fitar da jawabi ta bakin Mai taimaka masa wajen yada labarai da hulda da jama’a, Dr. Umar Jibrilu Gwandu a ranar Lahadi, 13 ga watan Maris 2022.

Dr. Umar Gwandu ya ce akwai rashin fahimtar abin da Ministan ya fada a game da binciken da ake yi wa DCP Abba Kyari na hannu a badakalar Hushpuppi.

Gwandu ya ce Matsayar ofishin Ministan shari’a shi ne har yanzu ba a kai ga karshen binciken da ake yi ba a rashin hujjojin da aka samu dangane da rahoton farko.

Hadimin Ministan ya ce AGF ya yi kalamai ne domin a cigaba da gudanar da bincike domin a dauki matakin da ya kamata, ba kokarin wanke jami’in tsaron ba.

“Da alamu akwai rashin fahimtar wannan lamarin. Har yanzu bincike ake gudanarwa, don haka ofishin lauyan gwamnati ya bukaci a kara bincike.”

- Dr. Umar Jibrilu Gwandu

This Day ta rahoto Umar Jibrilu Gwandu yana mai cewa makasudin cigaba da binciken shi ne gano gaskiyar wasu abubuwa da har yanzu sun shige duhu.

Rahoton ya ce kawo yanzu, PSC ba ta karbi rahoton binciken da aka gudanar a kan zargin da ake yi wa Kyari da kuma samun shi da laifi da aka yi a Amurka ba.

Ina binciken da IGP ya yi?

Hukumar kula da aikin ‘yan sanda ba su karbi binciken IGP wanda Marigayi DIG Joseph Egbunike ya gudanar ba inda ya bada shawarar ragewa DCP Kyari matsayi.

Wata majiya tace ana sauraron ’yan sanda har yanzu, bayan an ba su makonni biyu su kammala bincikensu. Sai dai har yanzu ‘yan sanda ba su ce komai ba tukun.

DIG Joseph Egbunike ya mutu

Rahotanni sun bayyana cewa babban jami’in ‘dan sandan kasar nan, Joseph Egbunike ya rasu a makon jiya, makonni kadan bayan ya yi bincike a kan Abba Kyari.

Egbunike shi ne Mataimakin Sufeta-Janar na ‘yan sanda wanda yake kula da bangaren FCID. Marigayin yana cikin 'yan sandan kasar nan masu ilmi da sanin aiki.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN