Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kai sabon farmaki a garin Kebu da kewaye a Masarautar Zuru a jihar Kebbi sun kashe tsofaffi da jama'a


Yan bindiga sun mamaye garin Kebu da ke karamar hukumar Danko Wasagu a Masarautar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi suka farmaki jama'a ranar Talata 22 ga watan Maris 2022.  Shafin isyaku.com ya samo.

Rahotanni na cewa ana zargin Yan bindigan sun kashe wani kurma mai suna Dahiru a farmakin na ranar Talata kuma suka kora shanayen mahaifinsa masu yawan gaske tare da shanayen bayin Allah. Yan bindigan sun banka wa wasu gidaje wuta a rikon Kebu da ke kusa da garin Tadurga, tare da kone wani gonan rake.

Majiyarmu ta ce ana zargin Yan bindigan sun kashe mutum 4 ranar Litinin kuma wadanda suka kashe tsofaffi ne da suka samesu zaune ko kwance a cikin zaure domin basa iya gudu.

Har yanzu haka lokacin rubuta wannan rahotu Yan bindigan na yankin Kebu.

Karin bayani na nan tafe..... 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN