Da duminsa: Kotu ta wanke Kabiru Taraki daga zargin badakalar N715m bayan ya rugurguza hujjojin shaidun EFCC su 12 kan tuhume-tuhume 16 da aka yi masa a gaban kotu


Alkalin babbar Kotun tarayya da ke Abuja Justice Inyang Ekwo ya wanke tsohon Ministan ayyukan musamman Kabiru Turaki kan zargin badakalar N715m da hukumar EFCC ta gurfanar da shi a gaban Kotun. Shafin labarai na Jaridar isyaku.com ya samo.

Alkalin Kotun ranar Litinin 28 ga watan Maris 2022, ya ce hukumar EFCC ta kasa kare hujja ta shaidunta da ta gabatar kan zargin da take yi wa Turaki a jerin tuhume-tuhume har guda 16 da ta yi wa Turaki a gaban Kotun.

Ya ce EFCC  ta kasa gamsar da Kotu kan dalilin tuhuma da take yi wa Turaki. Ya ce Turaki ya rugurguje duk hujjojin shaidu har guda 12 da EFCC ta gabatar a gaban Kotu domin neman Kotu ta hukunta shi kan zargin badakalar makuddan miliyoyin Naira da ta yi zargin ya wawushe.

Ya ce a lokacin bibiyan shaidun da EFCC ta gabatar, Kotu ta gano cewa Turaki baya cikin wadanda suka sa hannu a matsayin amintattun mutane da ke iya sarrafa asusun ajiya na ma'aikatar lokacin da yake rike da mukamin Minista kuma bai bayar da umarni a tura wasu kudade zuwa asusunsa ba ko na kampaninsa saboda baya cikin Ministerial Tender Board, domin tun farko baya cikin Ministerial account signitory, sakamakon haka Alkalin Kotun ya sallami Turaki kuma ya wanke shi daga dukkan tuhume-tuhume guda 16 da hukumar EFCC ta yi masa a gaban Kotu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN