Kebbi: Yan ta'adda sun halaka suka kone kurmus sakamakon farmakin jirgin yaki da soji a garin Magama da ke Masarautar ZuruWani faifen bidiyo da ke yawatawa a intanet na zargin cewa jami'an tsaron soji sun halaka Yan ta'adda da dama tare da kone baburansu a garin Magaba da ke karamar hukumar Danko Wasagu a Masarautar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi.

Bidiyon ya nuna yadda babura 17 tare da Yan ta'adda da yawa suka kone kurmus, a wani hari da ake zaton na jirgin yakin soji ne kan Yan ta'addan.

An jiyo wani jami'in tsaro a faifen bidiyon Yana bayani da harshen turanci. 

Ya ce" Babura 17 da gawakin Yan yadda masu yawa sun kone"

Mun samo cewa wannan ya faru ne bayan kisan jami'an tsaro guda 19 da Yan ta'addan suka yi a garin Kanya ranar Talata, lamari da ya kara tayar da hankalin jama'ar Masarautar Zuru duba da cewa ranar Lahadi Yan ta'addan sun kashe Yan sa kai 63 a wani kwanton bauna da suka yi masu a cikin daji


Previous Post Next Post