An kula da Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi a cikin motarsa ta aiki tare da ditebansa da mutum daya ya shiga Sakatariyar Cabinet office ba tare da rakiyar motocin kariya na jami'an tsaro ba da misalin karfe 11 da yan mintoci na safiyar ranar Laraba 16 ga watan Maris a garin Birnin kebbi.
An gan wasu jami'an tsaro a kan babur da ake zargin cewa jami'an tsaronsa ne sun biyo motar zuwa cikin Cabinet office yan mintoci bayan ya isa ofishinsa.
Kazalika, yayin gani da ido domin tabbatarwa, an lura cewa bayan motar Mataimakin Gwamna, ba sauran motocin jami'an tsaro, na yan Jarida, da na Protocol da aka saba gani a wajen da ake ajiye motocin Mataimakin Gwamna idan ya shiga ofis a cabinet office.
Ina mafita ?
Sakamakon wani bincike da muka gudanar ya ce Gwamnatin jihar Kebbi tana ba Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi hakkinsa na harkar tsaron lafiyarsa kamar yadda ya kamata a bisa tsarin doka.
Manuniya ga matsalar tsaro a jihar Kebbi
Sakamakon tabarbarewar tsaro a jihar Kebbi, ya zama wajibi Gwamnatin jihar Kebbi tare da manyan jami'an tson jihar su lurar da Mataimakin Gwamna kan muhimmancin wadatar da kanshi da tsarin jami'an tsaro da aka sama masa bisa tsarin doka.
Zanga-zanga matan soji a barikin soji na Zuru da abin da ya faru a filin jirgin sama a garin Zuru ranar Laraba da ta gabata na iya zama barazana ga tsaron lafiyar Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi ko da a cikin garin Birnin kebbi ne wanda ya haifar da muhimmancin ganin shi kansa tare da iyalansa sun wadatu da tsaro kafin mulkinsu ya kare nan da shekara daya.