Type Here to Get Search Results !

Majalisa ta amince da kudurin takara ga yan takara masu zaman kansu


A yau Talata ne majalisar dattijai ta amince da kudirin doka mai lamba 58 da ke neman bai wa ‘yan takara masu zaman kansu damar tsayawa takara, The Nation ta ruwaito.

Kudurin zai shafi ‘yan takarar shugaban kasa, na gwamna, da ‘yan majalisun tarayya, da na majalisun jihohi, da na kananan hukumomi.

Sanatoci 94 ne suka yi rajistar kada kuri’a, 89 sun kada kuri’a amincewa yayin da 5 suka ki amincewa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Hakazalika, majalisar ta yi watsi da wani kudirin doka da ke neman bai wa ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje damar kada kuri’a a lokacin zabe.

Legit

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies