Majalisar dokoki tarayyar Najeriya ta zartar da dokar ba kananan hukumomi damar cin gashin kansu na kason kudinsu daga Gwamnatin tarayya.
Wannan ya biyo bayan wani gyara da suka yi a kundin tsarin mulki na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima da aka samar da damar yin amfani da asusu na bai daya da Gwamnatotin jihohi ke amfani wajen sarra kudin kananan hukumomi.
Dokar dai ta sami amincewa rinjayen sanatoci da yan Majalisar wakilai.
Kazalika an zartar da dokar ba Majalisar dokoki na jihohi da ma'aikatun sharia damar cin gashin kansu na kason kudinsu daga Gwamnatin tarayya.
Za a tura dokokin da Majalisar tarayya ta zartar zuwa Majalisar dokoki na jihoho domin yin muhawwara a kansu kafin tabbatarwa.
Rubuta ra ayin ka