Rundunar NSCDC reshen jihar Kebbi ta kama wani mutum mai suna Aminu Bello bisa zargin yi wa diyarshi yar shekara 13 mai suna Hafsat fyade. Jaridar isyaku.com ya samo.
Rahotanni sun ce wani mutum ne ya rada wa jami'an bayan ya yi zargin abin da ke faruwa.
Kakakin rundunar na jihar Kebbi DSC Akeema Babatunde Adeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
Ya ce za su gurfanar da wanda aka kama a gaban Kotu da zarar sun kammala bincike.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI