Kotu ta tasa keyar wata Yar shekara 20 da haihuwa mai suna Amina Umar zuwa Kurkuku bayan ta amsa tuhumar aikta kisan kai bayan ta kashe jaririn da ta haifa mai kwana uku da hauhuwa a Duniya. Shafin Jaridar isyaku.com ya samo.
Kakakin rundunar yansandan jihar Adamawa DSP Suleiman Yahaya Nguroje ya ce Amina ta ce ta kashe jaririn ne bayan ta gano cewa saurayinta da ya yi mata ciki ba zai iya daukar dawainiyarta da na jaririn ba.
Tun farko dai Amina ta kashe aurenta, ta koma tana soyayya da tsohon saurayinta wanda ke aikin kanikanci. Suna tsakar soyayya ne sai ta dauki ciki ba tare da an daura masu aure ba.
Shi dai bakaniken saurayinta yana da matarsa da suke zaman aure. Ganin Amina ta dauki ciki sai ya yi watsi da lamarinta. Sakamakon haka ta yi awon gaba ta aika wani yaro ya sayo mata maganin kashe bera.
Dubun Amina ya cika ne domin lokacin da take aika yaro ya sayo mata maganin kashe bera makwabta sun jiyo ta. Daga bisani ta ce wa makwabta jaririnta ya mutu. Nan take makwabta suka kai kara wajen yansanda.
Sakamakon binciken yansanda ya gano cewa Amina ta dura wa jaririn ruwan maganin kashe bera, lamari da ya yi sanadin mutuwar jaririn nan take.