Type Here to Get Search Results !

Yadda yarinya mai shekara 5 ta fuskanci wani bala'i a hannun mahaifiyarta, duba dalili


Wata mata mahaifiyar Yara biyu mai suna Tina Idoroyen ta tsoma hannun diyarta yar shekara 5 cikin zuwan zafi bisa zargin satar soyayyen kifi. Jaridar isyaku.com ya samo.

Tina tana zaune da yayanta biyu a gida mai lamba N02, Gregory Street, Ikot Ansa da ke birnin Calabar a jihar Cross River.

Tina Idoroyen tana sana'ar sayar da abinci ne. Bayanai sun ce ta soya yankan kifi gida 19 domin ta sayar tare da abincinta. Sai dai lokacin da ta dawo sai ta tarar saura kwaya daya kacal. Bayan ta gudanar da bincike ne sai ta gano cewa diyarta mai shekara 5 da haihuwa ce ta cinye kifin.

Sakamakon haka Tina ta tsoma hannun yarinyar cikin ruwan zafi wai domin ta ladabyar da ita.

Tuni dai yan karadin kare hakkin kananan yara a jihar Cross river suka fuskanci Tina sakamakon azabtar da diyarta ta hanyar kone hannayenta a cikin ruwan zafi. 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies