Ababe 13 da za ka kula idan matarka tana neman maza


Sakamakon wani bincike da muka samo a isyaku.com kan wasu halaye da magidanci zai kula matukar matarsa na cin amanarsa wajen neman maza a waje, ya nuna cewa akalla ba za a ketare wadannan halaye da muka zana a kasa ba.

1. Za ka kula da wanzuwar sabbin dabi'a na reni tsakaninka da ita. Ba girmamawa ba mutuntawa duk da cewa ka kare hakkinta na zamantakewar aure.

2. Za ta daina danuwarka da neman ka biya mata bukatar kwanciyar aure.

3. Za ta daina damunka da neman ka yi mata hidimar zamantakewar na aure da suka shafi dinki da sauran iie-iren wadannan bukatu na sutura.

4. Za ta dinga shirga kwalliya fiye da yadda take yi a can baya idan za ta fita daga gida.

5. Za ta canja salon tufafi daga irin wadanda ta saba sakawa zuwa wadanda za su matse jikinta. Ko wadanda suka fi na da tsada. Kuma za ta dinga fita da Gele marmakin Hijabi.

6. Za ta dinga yin hidima na kudi fiye da abin da ya saba shiga hannunta.

7. Za ta kalubalance ka kuma za ta tayar da fitina idan ka nemi ka san ta yaya take samun kudi da take sarrafawa.

8. Za ta dinga canja abinci sabanin abin da ka bukaci a dafa a gida zuwa irin wanda take son ta ci ko kana so ko baka so. Domin za ta gaya maka cewa ai kuÉ—inta ne ba naka ba.

9. Za ta dinga fita daga gida zuwa bukukuwa akai-akai ko da bikin ba dangin uba balle na uwa. Wasu bukukuwan da zata dinga zuwa ba a garin da kuke za ayi ba.

10. Za ta bijire maka da fitina idan ka nemi ka hanata zuwa biki.

11. Za ka kula cewa ta hadu da kawayen mata masu yin dan karen kwalliya, ga turare an fesa da kuma bijirewa da dabi'ar cin cingam ko yawan shan lemun kwalba da sauransu.

12. Za ta dinga yawan zargin ka da neman mata a ko da yaushe.

13. Za ta dinga yawan kebe kanta a gefe kuma ta dinga magana murya kasa kwarai, kuma za ta dinga yawan waiwayawa idan tana yin magana a wayar salula domin tabbatar da cewa wani baya kusa da ita.

Sanin gaibu sai Allah.

Wannan hasashe ne kawai.

Allah ya bamu zaman lafiya tare da iyalanmu ya kare mu daga sharrin Iblis.

Nazarin Malam Isyaku Garba Zuru

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN