Wani mutum dan shekara 21 mai suna Ramadhan Johnson ya gurfana a gaban wata Kotu a unguwar Milimani da ke Nairobi na kasar Kenya bisa zargin taba duwawun wata Mata ba tare da yardarta ba.
Ana zargin cewa Johnson ya aikata laifin ne a kan titin hanyar Murang’a ranar 10, ga watan Maris 2022.
Takardar zargin da aka yi wa Johnson ya ce matar da ya yi wa laifi tana kan hanyar mayar da Lemarta shagonta ne da ke kan hanyar kasuwanci na hanyar Murang’a, sai Johnson wanda yake tafiya a bayanta ya taba duwawunta.
Sakamakon haka wasu maza guda uku suka nufato ta domin su taba duwawunta ganin haka ya sa ta gudu.
Ta ce bayan aukuwar lamarin, ta nemo wasu dattijai suka je wajen Johnson suka nemi ya amsa laifinsa kuma ya ba ta hakuri domin zancen ya kare. Sai dai Johnson ya ki. Sakamakon haka magana ta kai wajen yansanda, daga bisani suka gurfanar da shi a gaban Kotu.