Fusatattun jama'a sun aika wani saurayi mai suna Mendie lahira kuma suka banka wa gawarsa wuta sakamakon zargin satar Ayaban plantain a jihar Alwa-Ibom. Jaridar isyaku.com ya samo.
Wannan lamarin ya faru ne da safiyar ranar Juma'a 4 ga watan Maris a kan hanyar Umuahia da ke karamar hukumar Ikot Ekpene a jihar Alwa-Ibom.
Kafin mutuwarsa, Mendie ya shahara wajen addabar jama'a da sace-sace, lamari da ya sa aka taba daure shi a Kurkuku har tsawon shekara uku.
Sai dai bayan ya fito ne daga Kurkuku a bara, sai halinsa ya kara jagulewa. Ya zama gawurtaccen barawo.
Jama'a sun kashe shi suka banka wa gawarsa wuta bayan ya saci plantain.