Type Here to Get Search Results !

Yadda wata budurwa mai al'aurar maza da mata ta sami mijin aure, duba yadda lamarin ya kasance


Wata ‘yar Najeriya mai suna Mystique Evolving ta yi bayani koma-bayan yadda mutane suka yarda da cewa Ubangiji maza da mata kadai ya halitta, inda tace ya halicci mata-maza.

An haifi matar da al’aurar namiji da ta mace. Labarin Mystique Evolving ya yadu a 2019 bayan BBC News Pidgin ta yi hira da ita inda ta bayyana kalubalen da take fuskanta a matsayin ta na mata-maza.

A tattaunawar, matar cike da hawaye ta bayyana yadda ‘yan uwa da sauran jama’a suke kyamatar ta, wanda hakan ya sa take rayuwa a kebance fiye da shekaru 10 da suka gabata.

Mystique ta bayyana yadda ‘yan uwanta suka taba zane ta akan halin da take ciki.

Ta hadu da masoyinta na gaskiya

Bayan shekaru 3 da labarin ta ya yi ta yawo, ba masoyi kadai ta hadu da shi ba, har mijin aure ta samu sannan ‘yan uwanta sun dawo gare ta inda ta yi aure a shekarar 2021.

Bayan rungumar halin da take ciki da hannu bibbiyu, matar ta bayyana yadda take alfahari da yadda Ubangiji ya halicce ta a mata-maza.

Yanzu haka ita ce shugaban kungiyar lafiya ta Dynamic Initiative da kuma kare hakkin bil’adama, kungiyar da ke wayar da kai akan jinsi.

A tattaunawar da BBC News Pidgin ta yi da ita kwanannan, Mystique ta ce halin da ta shiga a matsayin ta na mata-maza ya nuna mata cewa mutum zai iya samun masoyin shi duk halin da yake ciki.

Ta koka akan yadda ake nuna wa mata-maza rashin tausayi a Najeriya inda tace akwai masu irin halittar ta a kasar nan.

Legit

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies