Type Here to Get Search Results !

Wuta ta kone dan bunburutu da matarsa kurmus, duba dalili


Wahalar mai da ake fama da shi a fadin tarayya ta yi sanadin mutuwar wani dan kasuwar bayan fagge, wadanda akafi sani da 'yan bunburutu' da matarsa a garin Jos.

Miji da matan sun mutu ne ranar Alhamis yayinda wuta ta tashi cikin dakin girkinsu inda mijin mai suna Gideon Pam yayi ajiyan jarkokin man fetur a unguwar Zawan, karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Plateau.

Wata makwabciyarsu, Miss Shantel Alphonsus, ta bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) cewa Gideon na sayar da mai ta bayan fagge a Zawan.

Tace:

"Da safe aka kira shi cewa ya zo ya karbi mai daga gidan mai, sai ya koma gida ya debo jarkoki."

"Yayinda yake kokarin juye feturin dake cikin jarkokin, kawai sai wuta ya tashi cikin Kitchen din da ya ajiye jarkokin."

"Matarsa Mercy ta shiga kitchen din ceton mijinta amma wutar ta ritsa da ita."

Miss Shantel ta bayyana cewa basu dade da haihuwan sabon jariri ba.

Diraktan hukumar kashe gobara na jihar Plateau, Caled Polit, ya tabbatar da lamarin kuma yayi Alla-wadai kan yadda wutar ta babbakasu kafin jami'an kwana-kwana su iso.

Legit

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies