Type Here to Get Search Results !

Daga karshe uwar kungiyar Yan Jaridar ta kasa NUJ, ta amince da zaben Garba Muhammad Yeldu a matsayin Mataimakin shugaban kungiyar a jihar kebbi


Uwar kungiyar Yan Jarida na kasa Nigerian Union of Journalists NUJ ta amince da zaben Garba Muhammad Yeldu a matsayin Mataimakin shugaban kungiyar yan Jarida na kasa reshen jihar Kebbi.

Biyo bayan wata takarda da uwar kungiyar ta kasa ta fitar kuma ta aike wa Garba Muhammed Yeldu na Kebbi radio ranar 24 ga watan Maris, wanda sakataren kungiyar na kasa ya sanya wa hannu. Takardar ta tabbatar da amincewa da  Garba a matsayin Mataimakin shugaban yan Jarida a jihar Kebbi.

Idan baku manta ba, mun labarta maku yadda takaddama ta taso biyo bayan rantsar da Usman Abdullahi Shehu da aka yi a matsayin Mataimakin shugaban yan Jarida na kasa reshen jihar Kebbi.

Lamari da ya janyo ce-ce-ku-ce da kalubale da amanar dunkulewar kungiyar tsintsiya madaurinki daya.

Biyo bayan bincike da uwar kungiyar ta kasa ta gudanar kan yadda aka gudanar da zaben da kuma tarin bayanai da ta samu, daga karshe uwar kungiyar ta kasa ta amince da zaben da aka yi wa Garba Muhammad Yeldu a matsayin Mataimakin shugaban kungiyar yan Jarida reshen jihar Kebbi. 


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies