Yan wata kungiyar asiri masu gaba da juna sun yi wa wani saurayi dan kungiyar asiri ta Bobos mai suna Christopher Samuel kisar gilla a bainar jama'a kuma suka banka wa gawarsa wuta a jihar Bayelsa.
Lamarin ya faru ne ranar Lahadi bayan mumunan rikici ya kaure tsakanin bangarorin kungiyoyin asiri a Unguwar Swali da ke birnin Yenagoa babbar birnin jihar Bayelsa.
Yan kungiyar asiri na daya bangaren sun kashe Samuel kuma suka kone gawarsa. Kakakin hukumar yansandan jihar Bayelsa ya tabbatar da aukuwar lamarin.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI