Akalla dalibai hudu sun mutu bayan ginin makarantarsu da ke dauke da ajin karatu da dama ya rufta a makarantar Diamond Grammar College da ke garin Ikang a karkashin karamar hukumar Bakassi a jihar Cross River. Jaridar isyaku.com ya samo.
SaharaReporters ta ruwaito cewa ginin ya rufta ne lokacin da daliban ke tsakar rubuta jarabawa ranar Juma'a .
Yayin da dalibai biyu suka mutu nan take ranar da lamarin ya faru ranar Juma'a , sauran dalibai biyu sun mutu ranar Litinin 28 ga watan Maris yayin da suke jinya a asibiti.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI