Jami'an tsaro 7 sun rasa rayukansu yayin fafatawa da 'yan bindiga a Neja


Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Neja ta tabbatar da mutuwar jami’an tsaro akalla 7, ciki har da baturen ‘yan sanda da ke kula da yankin Nasko a karamar hukumar Magama.

Kakakin ‘yan sanda a jihar ta Neja DSP Wasi’u Abiodun ya ce jami’an tsaron da suka rasa rayukansu yayin fafatawa da ‘yan bindigar sun hada da ‘yan sanda biyu, ‘yan Vigilante 4, sai kuma Baturen ‘yan sandan yankin Nasko.

Bayanai sun ce anyi musayar wuta tsakanin jami’an tsaron da ‘yan ta’addan ne da tsakar ranar Talatar nan, bayan da ‘yan bindigar suka yi yunkurin kai mummunan hari a garin Nasko.

Neja da ke yankin arewa maso tsakiyar Najeriya, na daga cikin jihohin kasar masu fama da hare-haren ‘yan bindiga wadanda gwamnati tayi shelar bayyana su a matsayin ‘yan ta’adda.

Baya ga barazanar ta ‘yan fashin daji ko barayin shanu da ke kisa da satar mutane domin kudin fansa, Neja na fuskantar barazanar wani tsagi na mayakan Boko Haram da raotanni suka ce sun yi kaka gida a wasu yankunan jihar.

rfi

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN