Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 1 ga watan Maris, ya bukaci majalisar dokokin kasar nan da ta yi wa sabuwar dokar zabe ta 2022 da aka sanya wa hannu kwaskwarima.
A wata wasika daga fadar shugaban kasa da shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan ya karanta yau Talata, shugaba Buhari ya shaidawa majalisar dokokin kasar da ta duba batun cire sashe na 84 (12) gaba daya.
Wannan bangare na dokar zabe ya tanadi doka kan masu rike da mukaman siyasa da su yi murabus daga ofishinsu kafin su yi takarar fidda gwani a jam’iyyunsu na siyasa, inji rahoton Punch.
A cewar shugaban, tanadin dokar ta sashe na 84 (12 ) ta saba wa hakkin wadanda ke rike da madafun iko.
Karin bayani na nan tafe...
Source: Legit.ng
Rubuta ra ayin ka