Wata Kotun Majistare mai zamanta a birnin Akure ta tasa keyar wani matashi dan shekara 23 mai suna Victor Akinwa zuwa kurkiuku bisa zargin kashe mahaifinsa mai sun Justus.
Mai gabatar da kara na yansanda ya gaya wa Alkalin Kotun Majistare cewa Victor ya yi amfani da tabarya ne ya buge mahaifinsa. Sakmkon haka mahaifinsa ya rasa ransa.
Ya ce lamarin ya faru ne a gidan mahaifinsa da ke Basi Road a garin Udanre da ke karamar hukumar Udanre na jihar Ogun.
Bayan sauraron karar, Alkalin Kotun Mr. Damilola Sekoni, ya tasa keyar Victor zuwa Kurkukun garin Olokuta, ya kuma dage karar zuwa ranar 30 ga watan Maris 2022 domin ci gaba da sauraron shari'ar.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI