Da duminsa: Fusatattun matasa sun yi wa wata mata dukan ajali a bainar jama'a a cikin garinsu, duba dalili


An kashe wata mata mai suna Chukwuwezu da kuka bisa zargin maita a jihar Delta.

Jaridar isyaku.com ya samo cewa lamarin ya faru ne a  Mbiri Kingdom da ke karamar hukumar Ika North East da ke jihar Delta a karshen mako.

Wani ganau ya ce an fara dukan matar ne kan hanyarsu ta zuwa caji ofis, saboda basaraken garin Obi baya nan. Sai dai wani hatsabibin mutum mai  suna Mr Chukwuekwu ne ya zuga jama'a har suka kashe matar bayan wani dansanda ya yi kokarin hana jama'a kashe matar amma lamarin ya ci tura.

An bar gawar matar a filin gari da ake kira Market square. Sai dai daga bisani Jami'ai sun dauke gawarta suka tafi da ita asibiti yayin da ake ci gaba da bincike. 

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN