Wanda ake tuhumar mazaunin Goron Dutse Quarters Kano, yana fuskantar tuhuma guda biyu da suka hada da zamba cikin aminci da damfara, Daily Trust ta ruwaito.
Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Sifeta Abdullahi Wada, ya shaida wa kotun cewa wanda ya shigar da karar, Jamilu Ibrahim na Galandanci Quarters, ya kai kara ofishin ‘yan sanda na Sabon Gari a ranar 10 ga watan Maris.
Sifeta Wada ya ce wanda ya shigar da karar ya bayyana cewa, ya bai wa Ado kwalaye 260 na kayan dandano, wato Maggi da ya ajiye masa a shagonsa, kuma a lokacin da ya je daukar kayansa ya gano cewa kwalayen Maggin guda 22 da kudinsu ya kai N216,000 sun yi batan dabo.
Wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, Daily Trust ta ruwaito.
Alkalin kotun, Dakta Bello Khalid, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake kara sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Afrilu.
Legit
Rubuta ra ayin ka