Za a fara sanyawa 'yan sandan Najeriya kyamara domin naɗar aikace-aikacensu



Majalisar wakilaii a Najeriya ta buƙaci gwamnatin ƙasar ta samar da kyamarorin da za a riƙa ɗaurawa a jikin jami'an tsaro, kuma a kafa cibiyoyin sa ido a kan aikace-aikacensu a faɗin ƙasar.

A cewar majalisar sanya wa jami'an tsaro kyamarori, zai taimaka wajen rage ƙorafe-ƙorafen keta haƙƙin ɗan adam da kuma tozarta ikon da doka ta ba su.

Hon. Abubakar Yunus, ɗan majalisar wakilai ne a Najeriya ya kuma shaidawa BBC cewa dalilin daukar wannan matakin, shi ne yadda korafe-korafe suka yi yawa kan jami'an 'yan sandan kasar ta fuskar amfani da karfi fiye da kima ga farar hula.

''Ana son tabbatar da aiki ingantacce, kuma bisa tsari ba tare da wata kumbiya-kumbiya da cuku-cuku irin na jami'an tsaro, wannan shi ne abin da wannan doka ta ke son kawarwa.

Babban dalilin da ya sanya muke so yin hakan a wanna zamani shi ne tuhume-tuhume sun yi yawa kan 'yan sandan Najeriya, wanda ake ganin su na kisa ba gaira ba dalili, kuma yawanci idan abu ya faru sai ka ji sun ce wai an yi domin tsare kan su,'' in ji Honarabul Yunus.

Ya kara da cewa a wasu lokutan za a ga jami'an kwastam sun harbe mutum, ko jami'an 'yan sanda a wurin binciken ababen hawa su harbe mutum, da dai sauran lamura da ke faruwa irin hakan.

Wadannan na daga cikin dalilan da majalisa ta kawo dokar ta yadda idan suka aikata wannan kamarar da ke jikinsu za ta nadi duk wani motsinsu ta yadda za a san halin da suke ciki a wuraren aiki.

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

An dai dade ana zarge-zargen 'yan sanda na cin zarafi da tozarta farar hula, ind wasu ke ganin tuntuni ya kamata a dauki mataki irin wannan.

Amma Honarabul Yunus ya ce an dauki matakin ne saboda babban kalubalen da Najeriya ke fuskanta da ba a taba zaton za a samu kai a ciki ba wato matsalar tsaro.

''Misali rikicin Boko Haram, sai kuma ta 'yan fashin daji, da barayi mutane domin neman kudin fansa, da makamantansu, sai muka lura su jami'an tsaro da za su kare hakkin dan adam ana tuhumarsu da ketawa.

Waɗannan dalili suka sa muka ga dacewar yin hakan sanna baki ya zo ɗaya akan wannan kuduri sannan dukkan majalisa sun amince da shi ba tare da wani ja-in-ja ba.''

Yunus ya ce nan ba da jimawa ba za a fara ganin wannan doka ta fara aiki, kuma an yi nasara ta fado bangaren da majalisa ke bai wa shawara, sannan za mu tabbatar wannan shawara da dokar za ta kai ga kwamitin da ke tabbatar da doka domin ganin an fara amfani da ita ba tare da bata lokaci ba.

Su na kuma fatan ganin da zarar kwamitin ya zauna ya yi nazari akai ba zai dauki lokaci ba za a zartar da shi.

Ko a shekarar 2020 sai da matasan Najeriya suka jagoranci gagarumar zanga-zangar ƙyamatar kisa da cin zalin da ƴan sanda ke yi a Najeriya.

BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN