Barawo ya sace kudi a POS, kudan zuma sun tilasta ya tona wa kansa asiri, duba yadda ta faru


Wani abin mamaki ya faru bayan wani mutum da ya saci kudi a wani POS ya dawo da shaidar abin da ya sata washegari kuna cikin matsanancin hali na damuwa, azaba, da kunci. Jaridar isyaku.com ya samo.

Lamarin ya faru a yankin APAC a gundumar Kaberamaido da ke gabacin kasar Uganda.

Rahotanni na cewa bayan an yi wa mai POS sata, ya je ya kai kara wajen wani Boka

Sai dai washe gari kwatsam sai ga wanda ya yi satar dauke da sauran abin da ya sata. Kuma yana cikin kunci domin dai kudan zuma sun daskare a bayansa.

Nan take aka sanar da yansanda domin kauce wa yiwuwar wasu su fada masa da duka har su kashe shi ko su yi masa illa, duba da yadda jama'a suka taru domin ganin abinda ke faruwa.

Sai dai Boka ya bukaci ala tilas a ba shi lokaci cewarsa wajibi ne ya gudanar da karkaren aikinsa domin sama wa barawon lafiya kafin  dauki kowane irin mataki.

Latsa kasa ka kalli bidiyo:

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=10221089883091834&id=1086336452

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN