Tap di jan: Wani mutum ya jefa yaro mai shekara 4 cikin rijiya domin ya sami rashin jituwa da mahaifin yaron


Alkalin kotun Majistare da ke zamanta a Kano, a ranar Juma'a, ya bada umurnin a tare wani mutum mai shekaru 33, Abubakar Aminu, a gidan gyaran hali kan zarginsa da jefa yaro dan shekara hudu, Abdulmalik Suleiman cikin rijiya.

An tuhumar wanda aka yi karar, mazaunin Rijiyar Lemo Quaters a Kano da laifin yunkurin aikata kisa kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Yadda abin ya faru

Mai gabatar da karar, Asma'u Ado, ta sanar da kotu cewa wani Aminu Suleiman mazaunin Bachirawa Quaters, a Kano ne ya kai rahoton afkuwar lamarin a ofishin yan sanda na Rijiyar Lemo a Kano a ranar 14 ga watan Oktoban 2021.

Ado ta ce yaron dan shekara hudu dan wanda ya yi korafin ne.

Ado ya yi ikirarin cewa a ranar, misalin karfe 2 na rana, wanda aka yi karar ya samu rashin jituwa da wanda ya yi karar, hakan yasa wanda aka yi karar ya jefa yaron cikin rijiya a Bachirawa Quaters da gangan.

Ya ce an ceto yaron sannan aka garzaya da shi Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad domin a yi masa magani, rahoton Vanguard.

Mai gabatar da karar ya ce laifin ya ci karo da sashi na 229 na dokar Penal Code.

Wanda ake zargi ya musanta laifin

Wanda aka yi karar ya musanta aikata laifin da ake tuhumansa.

Babban alkalin kotun, Mustapha Sa'ad-Datti, ya dage cigaba da sauraron karar har sai ranar 21 ga watan Fabrairu kamar yadda NAN ta rahoto.

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.

An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Yan sandan suna zarginsa da:

"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci".

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN