Wani Ango ya yi wa Amaryarsa duka yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa dakin daurin aure.
Rahotanni na cewa lamarin ya faru ne lokacin da Amarya ta fito daga shagon mai gyaran gashi.
Nan take Ango ya rufe ta da duka a kan wani dalili da ba a ambata ba a bainar jama'a.
Lamarin ya faru ne a Sultan Hussein Street da ke yankin Gwamnati a Ismailia na kasar Masar watau Egypt.
Sai dai rahotanni sun ce an ci gaba da shagulgula bayan an daura auren, kuma Ango da Amarya sun ce komai ya wuce domin sun sasanta kansu.
Kazalika sun saki Hotuna da bidiyon daurin auren nasu ga yan'uwa da abokan arziki.