Ababe 6 da salon siyasar Abubakar Malami SAN ya samar a jihar Kebbi



Sakamakon bincike da kwararrun masana suka gudanar bayan sa ido kan yan soshiyal midiya masu goyon bayan yan siyasa a jihar Kebbi, ya nuna cewa sashen Ministan shari'a kuma Antoni janar na Najeriya Abubakar Malami SAN sun fi nuna kwarewa, natsuwa da hakuri wajen isar da sakonninsu ga jama'ar jihar Kebbi.

Biyo bayan wani zama da aka gudanar ranar Alhamis a ofishin Seniora News Network a garin Birnin kebbi, kwararrun kan harkar bayar da labarai na zamani masu cikakken rijista masu zaman kansu, ya sami halartar kwararrun masana kamar Malam I. G. Abubakar da Malam M. M Sokoto kwararru kan ingizon yanar gizo da sarrafa fasahar amfanin kimiyyar yanar gizo wajen isar da sakonni ga jama'a a zamanance.

Sauran sun hada da J.B Habibu da Joseph Msheliya, sai Ezra Musa, Aishatu Abubakar, Maryam Imrana da B.J Doka.

Masanan sun yi itifaki a kan cewa yan midiya na Abubakar Malami suna gudanar da aikin isar da sakonni cikin kwarewa da hikima.

Kadan daga hujjojin da masanan suka duba kafin isa ga matsayarsu kan lamarin, sun yi la'akari da:

1. Martabar su kansu yan soshiyal midiya a idanun jama'ar da suke kokarin isar da sakonninsu zuwa garesu.

2. Mayar da hankali wajen isar da sakon alhairi daga Abubakar Malami zuwa ga jama'ar jihar Kebbi.

3. Sun kauce wa biya wa masu habaice-habaice marasa tsasiri don kariyar martabar Abubakar Malami.

4. Sun nisanta da kirkiro laifi da gangan ko cin zarafin kowane dan siyasa ko da baya son Abubakar Malami.

5. Suna aiki cikin da'a da ke nuna tsabtar manufa wajen tafiyar da ayyukansu da isar da sakon Abubakar Malami.

6. Yayin da wasu yan soshiyal midiya ke rura wutar kalaman masu gidajensu wajen kira ga aikata ash-sha, yan midiyan Abubakar Malami suna kira ga tafarkin alhairi da zaman lafiya.

Wadannan kadan kenan daga ababe da dama da aka kafa hujja da su.

Yayin da hakan ke gudana, kwararrun sun kula cewa hakan ya daga martabar Abubakar Malami SAN zuwa kaso 80% a martabar siyasar jihar Kebbi, rufewa ranar 15 ga watan Fabrairu 2022 shikamakin kididdigansu.

Abin da ke faruwa a fagen siyasar jihar Kebbi a soshiyal mediya


Masanan sun lura cewa matasa sun mayar da kafar soshiyal midiya fagen bambadanci, cin mutunci, kirkirar laifi da gangan da kuma nuna hassada a fili ga wasu yan siyasa, marmakin yin amfani da wannan fanni zuwa ga samar wa kansu alhairi da ci gaba wajen dogaro da kai.

Masanan sun ce idan aka ci gaba da wannan tsari, shakka babu wannan sashe zai kwashe kafafun sakonnin siyasar jihar Kebbi a mutunce cikin tsabta. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN