Type Here to Get Search Results !

Yanzu yanzu: An yi wa barawon yaro kamun kazan Kuku, duba yadda lamarin ya faru


Rundunar yansandan jihar Ogun ta kama wani mutum mai shekara 35 da haihuwa mai suna Sunday Alani sakamakon sace yarinya mai shekara daya da haihuwa a kauyen Atolashe da ke karamar hukumar Odede a jihar Ogun.

Yansanda daga ofishin Odeda sun ce Sunday ya sulale ya shiga harabar gida inda mahaifiyar yarinyar ta shagala da aikin toya gari da kosan rogo, ta bar yarinyar tana wasa, sai ya dauke ta ya fice daga gidan da gudu.

Sai dai wani mutum da ke wucewa ya kula da yadda Sunday ya fito da gudu daga gidan dauke da yarinyar. Kuma nan take ya ankarar da jama'a, lamari da ya sa mahaifiyar yarinyar ta fuskance shi.

Daga bisani Sunday ya gaya wa yansanda cewa yana tare da wasu mata biyu ne. Kuma idan ya yi nasarar sace yarinyar zai ba matan ne su kuma za su ba shi N80.000. Sai dai matan sun gudu.

Ya ce ya taba sace Yara biyu lokaci daban daban a unguwar Egbeda da Akute da ke jihar Ogun.

Kakakin hukumar yansandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce Kwamishinan yansandan jihar Ogun ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin a sashen CIID.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies