Siyasar Kebbi: Dan soshiyal midiya ya yi wa maciya shinkafar siyasar Kebbi walle, duba abin da ya ce


An jima ana rade radin cewa akwai tsami da bangaranci kan yadda lamurra ke tafiya a zauren masu cokalin cin shinkafar siyasar jihar Kebbi.

Yanzu kam bisa ga dukkan alamu tura ta fara kaiwa bango tunda har Yan soshiyal midiya sun fara tonon asiri kan wasu lamurra na cikin gida.

Yayin da ake zargin Yan soshiyal midiya da ake cin shinkafar siyasar jihar Kebbi tare da su, amma suka kasa tabuka komai wajen kare martabar ubannin gidan siyasarsu a rudanin siyasa na cikin gida da ya kunno kai. Sai kuma ga wasu sanannun sunaye suna kokawa da zargin rashin yi masu adalci.

Dan soshiyal midiya Yusha'u Nata'ala, ya yi zargi mai karfi da ya aika sako ga jama'ar jihar Kebbi. Ya kuma yi zargin cewa su kam sun tura mota amma an barsu da kakkaban kura bayan motar siyasa da suka tura ta tashi.

Karanta abin da Yusha'u ya wallafa a shafinsa na Facebook:

"Wannan Shirin Babu Alkhairi a cikinshi domin har zuwa yanzu Turancin Gwandu yana cigaba da Yakar Yaran Ibrahim Bagudu kuma duk inda wata dama take a cikin Gwamnati Turancin Gwandu baibari Yaron Ibrahim Bagudu yasameta kuma anata bada Kukaman Gwamnati Yaransa kawai kake ganin ana sakawa.

Bamu bakin cikin komai akaba kowa domin duk An Wahala ammadai ai Gwamnati bata Mutun guba bace da Yaransa. 

Kamin Yanzu akwai Gidaje dayawa da ake Siyasar APC ta Gwamnati Amma Yanzu Saboda komawa baya dukkan Siyasar APC ta Tsagin Gwamnati tadawo Gida daya.

Muna Kiraga Turancin Gwandu daya tuna cewa bashikadai Yayiwa Atiku Bagudu Camping ba kuma akwai Wadanda sukafishi wahala dashi da Yaranshi. Kuma muna Kira da atuna da wadannan dasuka Wahala ga Siyasar Atiku Bagudu 

A A Na'amare Jega  Kabiru Zubairu Aminu Abbakar Faruku Bala Gwandu Usman Adamu Aliero Mas'ud Labaran Gwandu Real Sani Twoeffect Yawuri Cmrd Urwatu Aliyu Abdulrahman Ibrahim Sahihi Bashar Bala Tasleem Zakeeh Kambaza Abdulmalik Aubandoma Nasiru Musa Maiyama Dadai Sauransu.

Dukkan Wadannan Mutane sun Wahala a Siyasar APC kuma Tsagin Gwamnati Amma yau Tunda suna Tareda Ibrahim Bagudu an maidasu gehe ba'a komai dasu kuma babu wani Taimako da akeyi musu.

Muna taya Yan uwanmu Yan Social Media Wadanda suka samu shiga cikin wasu tsare tsaren Gwamnati amma muna kira da aduba Sauran Mutane Wadanda suka Wahala a Siyasance".

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN