Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a sabon dokar zabe da yan Majalisar tarayya suka yi wa gayara na 2021.
Hadimin shugaba Buhari na musamman Bashir Ahmad ya sanar da haka a sakon Twitter ranar Juma'a 25 ga watan Fabrairu.
A cikin harshen turanci ya ruwaito a shafinsa na Twitter cewa:
"BREAKING: President Muhammadu Buhari has signed the Electoral Act Amendment Bill 2021 into law."
Shugaba Buhari ya rattaba hannu a sabuwar dokar da karfe 12:25 na rana lokacin wani takaitaccen biki a zaure Majalisar zartarwa da ke fadar shugaban kasa a birnin Abuja.
Rubuta ra ayin ka