Yanzu-yanzu: Yan iska sun yi wa yansanda wani mugun aiki yayin da suke bakin aikinsu, duba ka gani


Hankula sun tashi a ranar Alhamis a yayin da wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka bindige yan sanda uku har lahira a shingensu a Enugu.

Lamarin ya faru ne a kan timber junction, kusa da Maryland a karamar hukumar Enugu ta kudu kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

An gano kuma ce bata garin sun sace wata mata da direban ta a wurin.

Vanguard ta gano cewa wani direban Keke Napep ya jikkata sakamakon harsashin da miyagun suke ta harbawa daga bindigansu domin su firgita mutane.

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Enugu ya tabbatar da afkuwar lamarin duk da bai bada cikakken bayani ba.

Ya ce yan sanda sun bi sahun yan bindigan

Ya ce:

"Har yanzu ba mu gama tattara bayani dangane da afkuwar lamarin ba. Amma dai an tura jami'ai domin su bi sahun miyagun."

Dakaci karin bayani ...

Source: Legit.ng

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN