Rikici ya barke a unguwa Agbado a karamar hukumar Alimosho a Jihar Legas a ranar Juma'a da safe a yayin da bangarori biyu na kungiyar direbobi ta Najeriya, NURTW, suka kacame da fada a yankin.
Wasu da abin ya faru a gabansu sun tabbatarwa The Punch cewa masu ababen hawa da mutanen da ke wucewa a hanya sun tarwatse don su tsira da rayuwarsu.
An kuma ji harbe-harben bindiga a yayin rikicin da ya faru saboda karbar tikiti a tashohin mota.
Saurari karin bayani ...
Source: Legit.ng
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI