Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a gidan mashahurin Malamin addinin Musulunci Dr Ahmad Gumi (Bidiyo)


Wani faifen bidiyo da ke yawatawa a intanet ya nuna wani sashe na gidan shahararren Malamin Addinin Musulunci Dr Ahmad Mahmud Gummi ya kama da wuta a Kaduna.

Bidiyon, wanda ya samo asali daga shafin Facebook na Dr Ahmad Gumi, ya nuna yadda jama'a da Jami'ai suka dukufa wajen kashe gobarar.

An gano jama'a tsaye suna Jaje wasu kuma sun dukufa wajen aikin ceton kashe wutar.

Bisa alamu da suka bayyana an shawo kan gobarar.

Kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani kan musabbabin tashin wutar ko kiyasin adadin asara da gobarar ta haifar.

Allah ya kara kiyayewa... 

Latsa nan ka kalli bidiyo

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN