Type Here to Get Search Results !

Yunkurin sake farmakin NDA: Jirgin yaki ya dagargaza yan bindiga fiye da 20 kan babura fiye da 50, ya jikita da dama a cikin daji, duba ka gani


Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa akalla Yan bindiga 20 ne suka mutu lokacin da suke kan hanyarsu ta shiga makarantar soji na NDA ranar Alhamis 10 ga watan Fabrairu sakamakon luguden wutan jirgin sojin sama. Jaridar isyaku.com ya wallafa.

PR Nigeria ta ruwaito cewa Yan bindigan na tafe ne a kan babura fiye da 50 kuma suka doshi makarantar ta horar da hafsoshin soji NDA. Yan watannin baya dai yan bindigan sun farmaki makarantar.

An katse wa yan bindigan hanzari ne bayan samun rahotannin sirri na gaggawa.

Nan take aka tura jiragen yaki masu saukar ungulu na sojin sama na Najeriya kuma suka tare yan bindigan suka yi masu luguden wuta. Nan take Yan bindiga 20 suka mutu saura suka jikata.

Yan bindigan sun baro kauyen Damari ne da ke karamar hukumar Birninn Gwari a jihar Kaduna kuma jiragen yakin soji suka katse masu hanzari kafin su isa NDA.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies