Jami'an yansandan shiyar Kemta ne suka kama ma'auratan a gidansu da ke lamba.72 MKO Abiola way, Leme Abeokuta, bayan Baale na al'umman Leme mai suna Moshood Ogunwolu ya kai kara wajen yansanda bayan an dinga jiyo mugun wari yana busowa daga dakin ma'auratan.
Sakamakon haka DPO na yansandan Kemta Division, CSP Adeniyi Adekunle, ya jagorancin jami'ansa zuwa gidan ma'auratan inda suka gudanar da bincike kuma aka gano sassan bil'adama a dakin maauratan.
Yansanda na ci gaba da gudanar da bincike kasancewa ma'auratan sun ce wani mutum ne ya kawo masu sassan jikin Dan Adam domin gudanar da tsafi saboda su matsafa ne.
Rubuta ra ayin ka