Da duminsa: Yan bindiga sun farmaki Masarautar Zuru a jihar Kebbi sun tafka mumunan aiki a garin Kanya da kauyukan kewaye


Kimanin Yan bindiga 300 Kan babura sun farmaki wasu kauyuka suka aikata mumunan ta'asa a kasar Zuru ranar Asabar 19 ga watan Fabrairu.

Rahotanni na cewa yan bindigan sun farmaki yankin ne da misalin karfe 2 na rana, kuma sun fara kai farmaki kan bayin Allah tun daga garin Kangon Wasagu zuwa Kanya har wucewa zuwa garin Zuttu, kauyen Mashekari da Dgoga, Komdunku da sauran kauyukan yankin.

Wannan lamari ya jefa jama'ar kauyukan wannan yanki cikin tashin hankali. Lamari da ya tilasta su samun mafaka a garin Kanya. Wata majiya ta tabbatar mana cewa har zuwa karfe 10 na dare ranar Asabar 19 ga watan Fabrairu, wasu jama'a daga kauyukan da ke kewaye da garin Kanya suna gudun hijira a cikin garin Kanya inda suka sami mafaka. Suna fargaban komawa gidajensu a kauyukansu cikin wannan yanayi saboda dalilan tsaron lafiya da rayukansu. 

Kazalika mun samo cewa an tabbatar da mutuwar mutum uku a halin yanzu, ciki har da wani fitaccen mutum mai suna Luka Mai katifa, bayan sun yi masa kwanton bauna suka kashe shi a yankin Zuttu.

Sai dai wata majiya ta yi zargin cewa adadin wadanda aka kashe a harin na ranar Asabar sun zarce adadin da aka ambata. Kazalika majiyar ta ce da yake ana cikin tashin hankali a wannan yankin a halin yanzu, sakamakon haka ake ci gaba da hada bayanai kan adadin mutane da aka kashe ko aka yi garkuwa da su, da adadin gidaje da aka kone da yawan shanaye da suka sace. 

Mun tattaro cewa yan bindigan sun yi kone konen dukiyan bayin Allah tun kusan mako daya da suka zafafa farmakin da suke kaiwa musamman yankin Danko Wasagu da ke Masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi.

Yanzu dai yan bindiga sun jera tsawon wasu kwanaki suna addabar kudancin jihar Kebbi ba kakkautawa, lamari da ya shafi yankin Koko zuwa Yauri karashe zuwa yankin Zuru.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN