Tsohon Sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya, Shehu Sani, ya bada labarin abin ya auku lokacin da suka dauki hanyar zuwa Kebbi halartan daurin aure.
Shehu Sani wanda ya shahara da yin jawaban barkwanci a kafafen ra'ayi da sada zumunta ya bayyana cewa an basu shawaran kawai suyi addu'a su cigaba da tafiyar .
Shi kuwa bai bi wannan shawara ba, addu'a dai ya yi amma ya juya motarsa ya koma gida.
A sakon da ya daura shafinsa na Tuwita ranar Asabar, Shehu Sani yace:
"Muna hanyar zuwa Kebbi daurin aure, sai aka sanar da mu yan bindiga sun tare hanya."
"Wasu suka ce muyi addu'a su cigaba da tafiya. An yi addu'ar dani amma na juya na tafi gida."
Legit
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI