Type Here to Get Search Results !

Yakin Ukraine: Rasha ta shirya tsaf da makamin nukiliya mai suna 'shedan 2' da zai iya shafe kasa guda daga doron Duniya idan aka harba shi


Rahitanni da dumin dumi daga Nahiyar turai na cewa kasar Rasha ta shirya tsaf bayan gwaje gwaje domin yiwuwar amfani da sabon sumfurinta na nukiliya da ta kira "Satan 2 liquid fueled nuclear missile" wanda ke da karfin shafe kacokam kasa guda daga doron kasa idan aka harba shi.

Masana sun ce shakka babu Rasha za ta iya amfani da makaman kare dangi idan har kasashen Duniya suka takura mata ta hanyar kaddamar da matakin soji a kanta sakamakon rikicinta da kasar Ukraine.

Wannan yana zuwa ne bayan ikirari da shugaba Putin ya yi a shafinsa na Facebook cewa rasha za ta rayu duk da takunkumi da kasashen turai da Amurka suka saka mata. Ya ce daga karshe dai kasashen turai ne za su wahala sakamakon takunkumin. 

Ya ce a baya Rasha ta rayu da takunkumi da kasashen taron dangi suka kakaba mata, ya ce tarihi ne zai maimaita kansa domin Rasha za ta sha ko da takunkumin.


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies