Da duminsa: Dambe ya kaure a gidan mai na AP2 Birnin kebbiDambe ya kaure tsakanin wasu masu motoci da ke kokarin shan man fetur a gidan man AP2 da ke kan titin Sarki Haruna  a garin Birnin kebbi ranar Litinin.

Da misalin karfe 10:30 na safe ne damben ya kaure sakamakon gardama kan kai'dar layin shan mai tsakanin wani Dattijo mai mota kirar 404 pickup da wani direba mai mota kirar Toyota Sharon.

Nan take gardama ya kaure kuma har aka yi yunkurin ba hammata iska, wani har da yunkurin kwada wa dayan sheburin karfe, shi kuma ya tube rigarsa a bainar jama'a domin ya kece reni wajen yin dambe da Dattijo mai pickup.

Latsa kasa ka kalli bidiyo:

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=10221134056396139&id=1086336452

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN