Yadda za ka sami kudi a sabon shirin Facebook na maballin Reel


Yanzu haka Kamfanin Facebook ya shirya narkar da makudan kudade ga masu kirkirar gajerun bidiyo su daura kafar, kamfanin ya kaddamar da maballin Reel a Facebook, wanda ka iya zama kishiya ko kini ga Tik-Tok.

Meta, mamallakin Facebook, ya bayyana cewa Reels zai samu a mazuban kwakwalen na'urori masu amfani iOS da Android a cikin kasashe kusan 150 a fadin duniya domin 'yan kirkire su sami kudin shiga ta hanyar wannan sabon lamari.

Mamallakin kamfanin Facebook ya magantu kan kudaden shiga

Reels: Meta ya kirkiri hanyar da masu hawa Facebook za su ke samun na kashewa | Hoto:Mark Zuckerberg Source: UGC

A wani sako da ya fitar, kamfanin ya bayyana cewa yana daga cikin damammaki da yake samar wa 'yan kirkire na samun kudi har Naira miliyan 125.5 duk wata kan kallon bidiyoyinsu a kan Reels, wanda aka shirya narkar da kusan N415bn.

Kamfanin na fasaha, bugu da kari, ya ce ingantayyar za ta hada da samar da Reels a tsagin labarai, Reels a wurin kallon bidiyo da dai sauransu wurare a duniyar Facebook, hakan kuma zai ba da damar hade aike bidiyo tsakanin Facebook da Instagram don saukake yada bidiyoyi.

Romon da Facebook ya dafa wa masu kirkirar bidiyo

Facebook yana da niyyar habaka shirin ga karin kasashe domin masu kirkirar bidiyo su sami karin kudaden shiga don ci gaba da kirkirar bidiyo ga Reels da zai dace da al'ummominsu, kamar yadda Legit.ng ta tattaro.

Kamfanin ya ce:

"Gina kan zurfin gogewarmu na taimakawa 'yan kirkire su sami kudi mai ma'ana daga hajojinmu na tallace-tallace kamar In-Stream da Stars, muna kuma gina sabon zabin samun kudi kai tsaye a Facebook Reels ta hanyar raba kudaden shiga na talla da tallafi daga masoya."

A cewar Meta, zai fadada gwaje-gwajen tallace-tallace na Facebook Reels ga duk 'yan kirkire da ke Amurka, Kanada da Mexico da kuma zuwa karin kasashe a cikin makonni masu zuwa.

Nau'in tallace-tallace da zasu cika aljihun 'yan kirkire

Meta ya ce zai fara da nau'i biyu: tallace-tallacen allo da ka iya zama cikin bidiyo tare da dushi-dushin alama da kuma tsarin tambari, wanda 'yan kirkire za su iya makalawa a duk inda suka ga dama a jikin bidiyonsu na Facebook Reel.

Kamfanin ya ce wadannan nau'ikan tallace-tallacen da ba su da wata matsala za su kawo kudaden shiga ga masu kirkirar bidiyo.

Reels na Facebook zai fara aiki a Indiya, Mexico, Kanada, Amurka kuma ana samun su a Zimbabwe, Zambia, Uganda da Tanzaniya.

Sauran kasashen sun hada da Swaziland, Afirka ta Kudu, Seychelles, Senegal, Rwanda, Najeriya, Namibiya, Mali, Malawi, Lesotho, Kenya, Guinea, Cape Verde, Kamaru da Burkina Faso.

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

A wani labarin daban, Mark Zuckerberg, ya ce bai damu da kudin da ya rasa ba ko kuma yawan masu amfani da suka yi hijira zuwa wasu kafofin sada zumunta yayin da hajojinsa suka daina aiki na tsawon sa'o'i bakwai a ranar Litinin, 4 ga Oktoba.

Zuckerberg, mai kamfanin Facebook wanda ya bayyana matsayinsa a shafin Facebook a ranar Talata, 6 ga Oktoba ya ce ya fi damuwa da wadanda ke dogaro da hajojinsa don cudanya da abokai da dangi.

Ya rubuta:

"Mun shafe awanni 24 da suka gabata muna bincike kan yadda za mu iya karfafa tsarinmu kan irin wannan gazawar. Wannan kuma tunatarwa ce ga yadda aikin mu yake da mahimmanci ga mutane.”

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN