Tap di jan: Wani matashi ya shake mahaifiyarsa har Lahira, duba dalili


A jiya Laraba, hukumar yan sanda reshen jihar Gombe ta jera wasu mutum takwas da ta kama da laifi daban-daban a faɗin jihar.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa ɗaya daga cikinsu, Garba Abubakar, ya shiga hannu ne bisa zargin shakare mahaifiyarsa, Salamatu Abubakar, yar shekara 45.

Kwamishinan yan sandan jihar Gombe, Ishola Babaita, ya ce wanda ake zargin ya yi wa mahaifiyarsa haka ne saboda ta masa faɗa ya daina shan miyagun kwayoyi.

Kwamishina ya ce:

"Wanda ake zargi ya shake mahaifiyarsa ne saboda ta masa faɗa ya dena ta'amali da miyagun kwayoyi. An yi gaggawar kai matar babban Asibitin Kumo, amma likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa."

"Ina shawartar iyaye su maida hankali da sa ido wajen kula da 'ya'yan su kuma su tabbatar ba su faɗa muguwar ɗabi'ar shan miyagun kwayoyi ba."

"Babban abun takaici wannan matar ta rasa rayuwarta a hannun ɗan da ta tsugunna ta haifa, ɗaya ne daga cikin sharrin kwayoyi."

Source: Legit.ng

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN