Rundunar yansandan jihar Ogun ranar 22 ga watan Fabrairu sun kama wata matar aure mai suna Ramota Bello bisa zargin kashe mijinta mai suna Bello Saliu. Shafin isyaku.com ya samo.
Dan'uwan mamacin ne ya kai karar Ramota wajen yansanda. Ya ce a ranar 12 ga watan Fabrairu, Ramota sun sami sabani da mijinta Bello. Sai dai bayan Bello ya yi barci. Sai Ramota ta tafasa ruwan zafi ta watsa masa.
Sakamakon haka aka garzaya zuwa asibiti da shi ranar 12 ga wata. Sai dai Bello ya rasu ranar 13 ga watan Fabrairu yayin da yake jinyar raunuka da ya samu.
Wannan mumunan lamarin ya faru ne a Unguwar Lafenwa da ke birnin Abeokuta.
Bayan mutuwar Bello, matarsa Ramota ta tsere ta boye a cikin gari. Sai dai ranar 22 ga watan Fabrairu an gano inda ta boye.
Sakamakon haka kanin Bello ya shigar da kara wajen yansanda wadanda nan take suka dira gidan da Ramota ta boye kuma suka damke ta suka tafi da ita ofishinsu.
Kakakin hukumar yansandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce Kwamishinan yansandan jihar Ogun ya ba da umarnin gudanar da binciken lamarin a sashen CIID domin ganin an gurfanar da Ramota a gaban Kotu.
Rubuta ra ayin ka