Yadda wani mutum ya cika bayan shakatawa da yarinya a cikin dakin Otal, duba yadda ta faru


Bayan shakatawa da yarinya, wani dan jihar Ribas ya cika a dakin Otal jiya ni mutumi yayi numfashinsa ta karshe a dakin Otal dake Ada George, karamar hukumar Obio-Akpor ta jihar Rivers bayan shakatawa da yarinya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan abu ya faru ne yan awanni bayan shigarsu cikin daki da yarinyar ranar Laraba.

Police

Bayan shakatawa da yarinya, wani dan jihar Ribas ya cika a dakin Otal jiya Laraba

Wani mutumi da ya ziyarci Otal din kuma ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa misalin karfe 2 na dare, yarinyar ta fito daga cikin dakin tana iwu tana neman dauki saboda mutumin da take tare da shi ya yanke jiki ya fadi.

A cewarsa, manajan Otal da masu gadi suka dira wajen kuma suka garzaya da shi asibiti.

An tattaro cewa an isa asibitin mutumin yace ga garinku.

Wani mai idon shaida wanda ya bukace a boye sunansa yace yarinyar ta bayyana yadda mutumin ya sha maganin karfin maza kafin suka shiga daki.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Grace Iringe-Kokom, ta tabbatar da labarin inda tace tuni an damke manajan Otal da yarinyar.

A cewarta:

"Lallai muna sane da abinda ya faru a Otal din kuma ana gudanar da bincike. Jami'anmu sun damke matar da Manajan Otal."

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN