Type Here to Get Search Results !

Saurayi ya kwankwadi fiya-fiya saboda budurwarsa za ta auri wani mai kudi a Kano, duba abin da ya biyo


Wani matashi a jihar Kano masi suna Tijjani Abubakar ya yi yunkurin hallaka kansa ta hanyar shan ruwan fiya-fiya ranar Talata, 15 ga watan Febrairu, 2022.

Tijjani, dan unguwar Gama a karamar hukumar Nasarawa ta jihar ya tsallake rijiya da baya.

City & Crime ta ruwaito cewa Tijjani ya yi kokarin hallaka kansa ne bayan budurwsa ta jizgashi don auren wani mutumi, wanda yafi kudi da iya soyayya.

DailyTrust ta ce wani mai idon shaida yace Abubakar mai sana'ar sayar da waya ne a Farm Center, ya sha da kyar bayan dan'uwansa ya gansa yana shan fiya-fiyan.

Yace:

"Yana ganinsa ya ruga da gudu, kuma tare da mutane suka samu damar kwace kwalbar fiya-fiyan dake hannunsa."

Dalilin da yasa nayi niyyar halaka kaina

Kalamansa na farko bayan farfadowa, Tijjani Abubuakar ya bayyana cewa ya yanke shawarar haka ne saboda ba zai iya rayuwa ba tare da ita ba.

Yace:

"An bani labarin tana shirin auren wani, kuma har ya tura magabatansa don ganawa da iyayenta. Shi yasa na yanke shawarar yin haka."

Source: Legit.ng

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies