Yadda saurayi mai shekara 22 ya sace wa Dattijuwa kuɗinta na garatuti baki daya


Yan sanda a Jihar Katsina, a ranar Litinin sun yi holen wani Aliyu Abdullahi mai shekaru 22, mazaunin Kasuwar Mata Street a Karamar Hukumar Funtua saboda damfarar wata tsohuwa.

Ya wawushe mata dukkan kudinta na garatuti ta hanyar amfani da katin ta na banki wato ATM inda ya siya mota da babur da kudin, Vanguard ta ruwaito.

Ba wannan bane karonsa na farko

An taba kama mayaudarin, wanda ya kware wurin damfarar mutane ta hanyar sauya musu katinsu na ATM a baya amma daga bisani ya fito daga gidan yari kuma ya cigaba da laifin.

Da aka tambaye shi kan yadda ya fito daga gidan yarin, Aliyu ya ce:

"Lauya na ne ya yi beli na bayan na shafe wata daya a gidan gyaran hali."

Aliyu, wanda a yanzu yana hannun yan sanda, ya amsa cewa ya sauya wa wata Maryam Sale, mai zaune a unguwar Sharar Pipes a Katsina katinta na ATM, ya cire kudin garatutinta da dukkan kudin da ta tara a rayuwanta kimanin Naira miliya daya da dubu dari takwas da dubu arba'in (N1,846,000).

Ya cigaba da cewa:

"Na tafi ATM don cire kudi sai ta zo a Keke Napep ta roke ni in cire mata kudi N10,000 dag asusunta ta hanyar amfani da ATM dina. Kafin in cire mata, na duba kudin da ke ciki sai naga akwai kudi masu yawa. Nan take na cire mata kudin amma na canja katinta da nawa. Bayan ta tafi, na wuce POS na fara cire kudi. Na yi kwana uku kafin na cire dukkan kudin da ke asusun."

Ya siya mota da babur da kudin

Da aka tambaye shi inda kudin suke, dan damfarar ya ce:

"Na siya mota, Henesy Accord kan N500,000 da kuma sabuwar babur kan N350,000 daga kudin, sauran kuma na yi ta kashe wa wurin siyan kananan abubuwa."

Legit

================

Daga Jaridar iyaku.com

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook fFacebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN