Wani jirgin sama mai saukar ungulu ya dauki Gwamna Abubakar Sani Bello na Neja a lokacin da ayarinsa ke makale a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ranar Lahadi, 31 ga watan Janairu, New Telegraph ta ruwaito.
Gwamnan dai da alama yana kan hanyarsa ta dawowa ne daga ziyarar ta'aziyyar Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamali, bisa rasuwar Hakimin Hammanu Dauda, a lokacin da cunkoso ya rutsa da shi.
Wani jirgin sama mai saukar ungulu ne ya dauki Abubakar daga kan hanyar yayin da sauran matafiya suka makale a kan babbar hanyar, kamar yadda ARISE News ta ruwaito a ranar Litinin.
Lokacin da manema labarai suka tuntubi babbar sakatariyar yada labaran gwamnan Mary Noel-Berje domin jin ta bakinta, ta yi alkawarin ba da bayani ta SMS, wanda har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba ta yi ba.
Titin Abuja zuwa Kaduna wanda ya zama mafakar ‘yan fashi da makami, na daya daga cikin hanyoyin da matafiya ke bi daga yankin Arewacin kasar nan zuwa kudanci.
Da yake magana kan musabbabin cunkoson ababen hawan, kakakin hukumar FRSC Bisi Kazeem ya bayyana cewa lamarin ya kara kamari ne bayan wani hadarin mota da ya afku a kan babbar hanyar.
Ya ce an baza jami’an hukumar FRSC akan hanyar domin sanya ido da kuma sassauta matsalar cunkoson.
Majalisar Wakilai ta Jihar Kaduna a watan Nuwamba 2021 ta nemi goyon bayan kawo karshen matsalar rashin tsaro a kan babbar hanyar.
Legit
================
Daga Jaridar iyaku.com
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakulabari
Facebook fFacebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka