Yadda miyagu suka shiga har gida suka halaka matar aure, suka raunata 'ya'yanta 2


Rukayya Mustafa matar aure ce mai shekaru 24 da aka shiga har gida aka halaka ta a yankin Dambare da ke jihar Kano.

Yankin Dambare ya na daga cikin yankunan da ke da makwabtaka da sabuwar jami'ar Bayero da ke Kano wacce ke kunshe da yawan daliban jami'ar, Daily Trust ta ruwaito.

City & Crime ta tattaro cewa matar da aka kashe har lahira an samu gawarta ne a gidanta da daren Asabar yayin da mijinta ba ya gida.

Miyagun sun nada wa 'ya'yanta biyu masu shekaru uku da daya dukan tsiya.

A yayin zantawa da City and Crime, kawun wacce aka kashen mai suna Kasim Ahmed, ya ce ya samu kiran gaggawa daga mijin wacce aka kashe wurin karfe 9 inda ya sanar masa aukuwa lamarin kuma suna hanyarsu ta zuwa asibitin Murtala inda aka tabbatar da mutuwarta.

"Ni ne waliyyinta, ni na bayar da auren ta. An kira ni yayin da nake gida aka sanar da ni cewa an kashe ta.

"A lokacin da na isa, na ganta a cikin mota kwance a mace. Har yanzu ba a san wadanda suka yi aika-aikar ba saboda a dakinta aka ganta kwance cikin jini. Allah ne kadai ya san abinda ya faru saboda jininta a daskare aka gani a jikinta.

"Abu na biyu, hannayenta sun kandare kuma ba su iya mikewa. Don haka babu wanda ya san abinda ya faru. Mijinta Jamilu Abdulkadir ne ya fara ganinta a cikin wannan halin yayin da ya koma gida da dare.

"Akwai tabarya wacce miyagun suka buga mata a kanta. Sun buge ta wurare biyu daban-daban. Sun doke dan ta mai shekaru uku da tabaryar wanda a halin yanzu bai san inda kanshi ya ke ba.

"Yaranta biyu ne kuma dayan shekararsa daya da watanni kadan."

Kamar yadda BBC ta ruwaito, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da aukuwar mummunan lamarin inda tace tana bincike a kai.

Mummunan al'amarin ya auku ne a garin Masaba da ke karamar hukumar Bursari ta jihar Yobe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Dungus Abdulkarim, ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata wurin karfe bakwai da rabi na dare.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN