Rahotanni na cewa Bello ya rudi yarinyar da N50 ta biyoshi zuwa dakinsa da ke gidajen ma'aikatan gidan yari na Yolde-Pate da ke karamar hukumar Yola ta kudu inda ya yi mata fyade.
Kakakin hukumar yansandan jihar Adamawa DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar wa manema labari faruwar lamarin.
Ya ce yansanda sun kama Bello kuma suna gudanar da bincike kan lamarin.
Wata hafsa mai suna Madam Laila, wacce ke sashen kare hakkin Dan Adam na Centre for Women and Adolescent Empowerment, ta ce an gudanar da bincike kan yarinyar kuma sakamakon binciken Asibiti ya tabbatar cewa an keta budurcinta.
Ta sha alwashin cewa za su bi diddigin shariar har zuwa karshensa domin ganin an yi wa yarinyar adalci.
Rubuta ra ayin ka