Yadda fusatattun jama'a sun babbaka wani mutum bisa zargin kone Al-qur'ani


Fusatattun jama'a sun kashe wani bawan Allah da ake zargi da kone Al-Qur'ani mai girma a kasar Pakistan.

An gano cewa jama'an sun lakada masa mugun duka tare da kona shi a garin mai suna Khanewal da ke lardin Punjab a kasar Pakistan, Aminiya Daily Trust ta wallafa.

Jama'a masu yawa ne a halin yanzu aka tabbatar da an kama su sakamakon hannunsu a kisan. Lamarin ya auku a ranar Asabar, kamar yadda Firayim minsitan kasar na harkokin addini, Tahir Ashrafi ya sanar.

Hakazalika, jami'an tsaro suna can suna cigaba da farautar sauran wadanda ke da hannu a kisan mutumin, Aminiya Daily Trust ta ruwaito.

Jami'an 'yan sanda a lardin sun ce a kalla an yi ram da mutum 15 da ke da hannu a cikin kisan kuma ana cigaba da farautar kusan tamanin da biyar.

Firayim ministan kasa, Imran Khan, ya bayar da umarni daukar tsatsauran mataki kan duk wanda ke da hannu a cikin barnar, daga ciki har da jami'an 'yan sandan da lamarin ya auku a kan idanunsu amma suka kasa yin komai.

"Za mu dauka mataki mai tsauri a kan wannan lamarin kuma za mu tabbatar da cewa doka ta yi halin ta. Ba zai yuwu mu kyale mutane su dinga daukar doka a hannunsu ba," cewar firayim ministan a wata muhimmiyar sanarwa.

Wannan kisan na zuwa ne kusan bayan wata 2 da aka nada wa wani manajan masana'anta dan kasar Sri Lanka mugun duka har ya mutu saboda zarginsa da aikata batanci.

Jama'ar sun tattaru ne a wani Masallaci a daren Asabar bayan dan wani limamin ya sanar da cewa ya ga wanda ake zargin ya na babbaka wasu shafukan Al-Qur'ani, a cewar Munawar Hussain, jami'in dan sanda da ke yankin.

A cewarsa, bayan 'yan sanda sun isa wurin, sun riski mutumin daddaure a jikin bishiya ba ya iya ko motsawa. Ya ce sun kansu 'yan sanda sai da jama'ar suka kai musu farmaki.

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, wadanda ake zargin sun tare da sace wasu matafiya kan babbar hanya kuma sun kai su wani makusancin daji.

Amma kuma cike da sa'a ga matafiyan, masu garkuwa da mutanen sun shiga hannun 'yan sa kai wadanda suka fito dasu daga dajin.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN